Majiyar watsa labaran kasar Masar a yau Laraba ta sanar da cewa: Shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi ba zai samu damar halattar zaman taron shugabannin kasashen musulmi mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da za a gudanar a kasar Turkiyya ba, don haka ministan harkokin wajen kasar ta Masar Samaha Shukri ne zai wakilci shugaban kasar ta Masar.
Majiyar ta kara da cewa; Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar Hisham Badar ne zai halacci zaman taron sharar fagen zaman taron shugabannin kungiyar ta kasashen musulmi ta OIC, inda a halin yanzu haka ma ya isa kasar ta Turkiyya.
Alaka tsakanin kasashen Masar da Turkiyya ta tabarbare ne sakamakon tsoma bakin da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdugan ke yi a harkokin cikin gidan Masar musamman goyon bayan kungiyar Ihwanul-Muslimin ta Muslim Brotherhood da aka kifar da gwamnatinsu a Masar. A gobe Alhamis ne za a bude zaman taron kungiyar kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a kasar ta Turkiyya.288